in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mutane dauke da makamai da ba a tantance su ba sun sace mataimakin jakadan Saliyo dake Najeriya
2016-07-02 14:33:17 cri
Wasu mutane dauke da makamai da ba tantance su ba sun yi awon gaba da mataimakin jakadan Saliyo dake Najeriya, janar Nelson William mai ritaya, a kan hanyar Abuja-Kaduna, a cewar wani jami'in tsaro.

Jami'in ya ce, mataimakin jakadan na shirin halartar wani bikin mika digiri ga daliban makarantar aikin soja AFCSC dake Jaji a jihar Kaduna.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo shi ma an gayyace wajen bikin mika digirin a Jaji.

Har yanzu hedkwatar 'yan sandan jihar ba ta tabbatar da wannan hadarin ba.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China