Ministan kwadago na kasar Chris Ngige, shi ne yayi wannan kira a Abuja, a lokacin da yake ganawa da shugabannin kungiyar dillalan man Najeriyar da jami'an kamfanonin mai na kasashen.
Ya ce an shirya tattaunawar ne da nufin lalibo bakin zaren warware matsalolin da kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas na kasar wato (PENGASSAN) da kuma kungiyar ma'aikatan mai da iskar gas na Najeriyar (NUPENG) inda suke zargin manyan dillalan mai na kasar da yunkurin sallamar ma'aikata.
PENGASSAN ta yi barazanar shiga yajin aiki na kasa baki daya, tun daga ranar 7 ga wannan wata, sakamakon zargin kamfanonin mai da iskar gas dake kasar na yin shelar sallamar ma'aikata.
Minsitan ya bukaci masu kamfanonin mai 'yan kasashen waje, da kada su mayar da korar ma'aikata a matsayin hanyar da zata warware matsalar komadar tattalin arzikin da suke fuskanta, ya bukace su dasu bi hanyoyin da doka ta tanada wajen warware wannan matsala.
Ngige, yace dokokin aikin kwadago zasu kare muradun dukkannin bangarorin biyu.(Ahmad Fagam)