in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Aljeriya ya alkawarta kyautata aiki da tsarin dimokaradiyya
2016-02-05 10:08:56 cri
Firaministan kasar Aljeriya Abdelmalek Sellal, ya sha alwashin ci gaba da kyautata aiki da tsarin dimokaradiyya a fadin kasar.

Mr. Sellal wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya kuma ja hankalin 'yan adawar kasar, game da aniyar gwamnatin kasar mai ci, ta amfani da kwaskwarimar da za a yiwa kundin mulkin kasar, wajen zurfafa aiki da salon mulki irin na dimokaradiyya.

Ya ce kudurin dokar gyaran fuska ga kundin mulkin kasar wanda shugaba Abdelaziz Bouteflika ya gabatar, na da nufin fadada 'yancin al'ummar kasar, da inganta harkokin jagoranci, da bin doka da oda, tare da karfafa 'yancin fannin shari'a.

Tun cikin shekarar 2011 lokacin da ake fuskantar juyin juya hali a wasu kasashen Larabawa ne dai shugaba Bouteflika ke kaddamar da sauye-sauyen siyasa a Aljeriya, inda kudurin yiwa kundin tsarin mulkin kasar ya kasance daya daga irin wadannan matakai da kasar ke gudanarwa a baya bayan nan.

Rahotanni sun nuna cewa sassan da za su fuskanci kwaskwarima sun hada da dokokin zabe, dana harkokin jam'iyyun siyasa, tare da na gudanar kungiyoyi da harkar yada labarai.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China