Sanarwar ta kara da cewa, wannan mutum mai suna Zahir Mehdaoui, dan shekara 29 ya zauna a birnin Brussels dake kasar Belgium, a yanzu kuma ana tsare da shi ne a gidan kaso, bisa zargin da ake masa na da alaka da ta'addanci. An ce Mehdaoui da daya daga maharan na birnin Paris Abdel hamid Abaaoud suna da alaka ta kusa.
A daren ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar 2015 ne aka kaddamar da hare-haren ta'addanci a birnin Paris dake kasar Faransa, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 130, tare da jikkatar wasu sama da 350. A kuma ranar 18 ga watan Nuwamba, a cikin matakin da bangaren 'yan sandan Faransa ya dauka, aka harbe Abdel har lahira, mutumin da ake zargi da kaddamar da harin ta'addancin na birnin Faris.(Bako)