in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya da Sin zasu hada gwiwa don hakar ma'adanai
2016-02-29 10:12:48 cri
A ranar Lahadin data gabata kasar Aljeriya ta bada sanarwar yin tattaunawa da kasar Sin domin yin hadin gwiwa wajen kafa wata babbar cibiyar ma'adinai mafi girma a kasar wacce ke arewacin Afrika.

Ministan al'amurran masana'antu da ma'adanai na kasar Abdesselam Bouchouareb, ya shedawa 'yan jaridu bayan kammala tattaunawa da babban jami'in kamfanin CCECC na kasar Sin Yuan Li cewar, za su hada kai da kasar Sin domin gudanar da aikin hakar ma'adanai a Gara Djebilet dake lardin Tindouf na kasar.

A cewar Bouchoureb, wannan shi ne karon farko da aka cimma daidaito game da batun aikin hakar ma'adinan na Gara Djebilet, dama dai tuni aka kammala yin bincike game da irin dunbun albarkatun kasar dake jibge a yankin.

Kamfanin dillancin labaran APS ya rawaito cewar, tuni shi ma ministan sufurin kasar Boudjemaa Talai, suka gana da mista Yuan, kuma sun cimma matsaya ne game da batun aikin gina layin dogo mai tsawon kilomita 950 wanda ya hada yankin na Gara Djebilet zuwa Abadla a lardin Bechar.

Gara Djebilet guda ne daga cikin manya wuraren hako ma'adinai a duniya wanda ke dauke da ton biliyan 3 da rabi na ma'adinin karafa.

Kasar Aljeriya tana bukatar yin amfani da wannan dama ne, domin kaucewa sayo karafu daga ketare. A shekarar da ta gabata, kasar ta kashe kimanin dala biliyan 10 wajen shigo da karafu daga kasashen ketare.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China