in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeriya tace tana goyon bayan yakin da Nigeriya take yi da ta'addanci
2016-01-30 12:51:46 cri
Kasar Algeriya a ranar Jumm'an nan ta sanar da goyon bayan ta ga Nigeriya a kokarin da take yin a yaki da ta'addanci, sakamakon harin da aka sake aiwatar wa a garin chibok na jihar Borno.

Bayan sace 'yan mata 219 a makarantar wannan gari a shekara ta 2014 , kungiyar 'yan ta'addan sun cigaba da kai hari a yankin arewa maso gabashin kasar ta hanyar kai munanan harin a kasuwar garin ta chibok, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Algeriya,Abdelaziz Benali Cherif ya sanar ma kamfanin dillancin labaran kasar APS.

Ya ce kasar ta Algeriya da kakkausar murya ta soki duk munanan ayyukan da yake dakushe kokarin gwamnati da al'ummar Nigeriya na dakile ta'addanci a yankin.

Ya kuma kara da cewar kasarsa zata cigaba da mara ma Nigeriya baya a yakin da take yi da wannan munanan ayyuka domin samar da tsaro a daukacin yankin domin al'ummar yankin baki daya.

Kafofin watsa labarai dai na kasar Nigeriya sun ruwaito sabbin hare-haren ta'addanci da aka yi a ranar laraba a Chibok wadanda suka hallaka akalla mutane 15 da soja daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China