in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sudan ta Kudu a kungiyar AU ya yi kira ga kasashen duniya da su kalubalanci jam'iyyar adawa da ta yi hadin gwiwa da gwamnatin kasar
2016-07-14 13:43:02 cri
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga jam'iyyar adawa, domin ta hada kai da gwamnatin kasar. Wakilin kasar Sudan ta Kudu a kungiyar AU, James Morgan shi ne ya bayyana hakan a jiya Laraba a yayin da yake halartar taron kolin kungiyar AU a birnin Kigali, babban birnin kasar Ruwanda,

James Morgan ya bayyana cewa, makomar Sudan ta Kudu ta dogaro ne ga jama'arta. A don haka kamata ya yi jam'iyyar adawa ta hada kai da gwamnatin kasar, domin a kara tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China