A nasu bangaren, manyan kusoshin kasashen Afirka dake halartar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU a Kigali na kasar Ruwanda, sun nuna damuwa kan yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu, tare da fatan ganin bangarorin kasar da ba sa ga maciji da juna zasu kawo karshen halin ja-in-ja da suke yi, da kiyaye yanayin tsagaita bude wuta, don maido da lumana a kasar tun da wuri.
Ban da haka kuma, masu halarta taron sun nuna yabo ga ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu. Louise Mushikiwabo, ministar harkokin wajen kasar Ruwanda ta ambaci batun mutuwar wasu sojojin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin a Sudan ta Kudu, inda ta ce, sojojin sun fi mai da hankali kan kare fararen hula maimakon tsaron kansu yayin da suka gudanar da aikinsu.(Bello Wang)