Wakilin kamfanin ayyukan ketare na Sin (COVEC) a Sudan ta Kudu, Zhang Biao ya bayyana cewa, a wannan rana, jiragen sama 3 sun tashi daga Nairobi zuwa Juba, domin dauke da ma'aikatan kamfanonin Sin, daga bisani sun koma birnin Nairobi da daren wannan rana.
A daren ranar Talata 12 ga wata, ma'aikatan kamfanonin Sin sama da 70 sun tashi daga birnin Juba zuwa Nairobi. An ba da labarin cewa, kawo yanzu akwai wasu sauran ma'aikatan Sin a Sudan ta Kudu.
Tun daga ranar 8 ga wata, sojojin dake karkashin jagorancin shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, da sojojin dake bin umurnin mataimakin shugaban kasar Riek Machar sun yi musayar wuta cikin tsanani a birnin Juba, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 272. Filin jiragen saman kasa da kasa na Juba ya taba daina aiki sakamakon wannan rikici. A daren ranar 11 ga wata, Salva Kiir da Riek Machar sun bada umurnin tsagaita bude wuta tsakaninsu.(Fatima)