in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu na kwarara zuwa Sudan
2016-07-14 10:42:59 cri
Gwamnatin kasar Sudan ta sanar a ranar Laraba cewa 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu da yawa na kwarara zuwa kasar Sudan sakamakon tashin hankalin da ya barke a Juba fadar mulikin kasar Sudan ta Kudu, kamar yadda jaridar Sudan Tribune ta bayyana a cikin wani rahotonta.

A ranar Alhamis da ta gabata, dakaru masu biyaya ga shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da masu goyon bayan mataimahin shugaban kasar Riek Machar, sun yi dauki ba dadi a tsakaninsu a kewayen fadar shugaban kasar dake birnin Juba, rikicin da ya fantsama zuwa sauran wurare da kuma kusa da filin saukar jiragen sama daga bisani.

Bisa rahoton da jaridar Sudan Tribune ta bayar, an rawaito kwamishina mai kula da aikin agaji na kasar Sudan mista Ahmed Mohamed Adam na cewa, a kwanakin baya an samu karin 'yan gudun hijira da suke kwararowa cikin kasar Sudan daga Sudan ta Kudu, sai dai har yanzu ba a iya tabbatar da ainihin yawansu ba.

Jami'in ya jaddada yadda kasarsa take cikin shiri domin tinkarar duk wata matsalar da za ta iya kunno kai ga 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu, idan rikici ya ki ci ya ki cinyewa a makwabciyar kasarsa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China