in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MINUSS ta yi kira ga shugabannin Sudan ta Kudu da su janye haramce haramcensu na kai da kawo
2016-07-13 10:42:32 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu (MINUSS) ta yi kira a ranar Talata ga shugabannin Sudan ta Kudu da su ba da umurni ga rukunonin sintiri na tawagar da su shiga wuraren da fararen hula suke don kare tsaronsu.

Da yake maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar suka sanar a ranar Talata, MINUSS ta bukaci dukkan bangarorin da su goyi bayan wannan mataki, da kuma baiwa fararen hula damar zuwa wuraren da za su samun mafaka cikin 'yanci, da janye haramce haramcen kai da kawo. Dole ne gwamnati ta rike nauyinta da kuma bude hanyoyi domin samar da sauki ga MDD da kungiyoyin ba da agajin jin kai don su ba da taimako ga fararen hula da rikicin ya shafa, da ba da damar kai mutane asibiti.

A cikin wata sanarwar da MINUSS ta bayar a Juba, an ce wannan ya hada daukar matakan gaggawa domin kare da sake bude filin jiragen saman kasa da kasa na Juba da farko. Rikicin ya fara a makon da ya gabata bayan gumurzu tsakanin dakarun gwamnati da dakaru masu adawa, wanda ya janyo mutuwar sojoji da dama da kara tsananta rikici a Juba.

Lamarin ya tsananta cikin mamaki a ranar Jumma'a, tare da janyo mutuwar daruruwan mutane. Bayan kura ta lafa a ranar Asabar, rikici ya sake barkewa a ranar Lahadi a dukkan fadin birnin, har zuwa ranar Litinin, sai aka sanar da tsagaita bude wuta.

Wakiliyar musammun ta sakatare janar na MDD, Ellen Margrette Loj ta kira ga Kiir da Machar dasu tabbatar da cewa an isar da sanarwar tsagaita bude wuta zuwa dukkan hedkwatocin jami'an tsaronsu domin ganin dukkan sojoji sun koma sansanoninsu, da dakatar da rikici tare da maido da doka da oda. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China