Tawagar ta hada da rukuni biyu na sojojin da kuna na ma'aikata da likitoci, adadin yawansu ya kai 225, kuma rukuni na biyu zai tashi a ranar 27 ga wannan watan.
Shugaban ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na yankin soja na Lanzhou na kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin shekara daya mai zuwa, sojojin kiyaye zaman lafiya za su zauna a yankin kudancin kasar Congo Kinshasa, wadanda za su gudanar da ayyukan gina hanyoyi da gadaje, ayyukan samar da ruwan sha da wutar lantarki da kiwon lafiya da sauran ayyukan jin kai a kasar. (Zainab)