in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya
2016-06-27 13:57:09 cri
A jiya da dare ne firaministan kasar Sin mista Li Keqiang, ya gana da mista Klaus Schwab, shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya, a birnin Tianjing dake bakin tekun kasar Sin.

A yayin ganawarsu, firaministan kasar Sin ya ce, tun bayan da aka kaddamar da dandalin tattaunawar Davos na lokacin zafi shekaru 10 da suka gabata, taron ya mayar da hankali wajen yin musayar ra'ayi tsakanin bangarorin Sin da kasashen waje, gami da hadin gwiwa tsakaninsu.

Taken dandadlin tattaunawar na wannan karo shi ne "Juyin-juya halin a fannin masana'antu karo na 4, kuma karfin da ya sa aka sauya salon da ake bi wajen raya masana'antu", wanda ya dace da muhimmin yanayin da ake ciki na samun babban ci gaban kimiyya da fasaha, da ci gaban yanayin masana'antu, don haka taron zai samar da ra'ayoyi masu amfani ga kasashe daban daban kan yunkurinsu na sauya tsare-tsaren tattalin arzikinsu.

A nasa bangaren, mista Klaus Schwab ya ce, akwai hulda mai kyau tsakanin dandanin tattaunawar tattalin arzikin duniya da bangaren kasar Sin, don haka dandalin tattaunawar, a karkashin jagorancinsa, zai yi kokarin tallafawa gwamnatin kasar Sin kan kokarinta na gudanar da gyare-gyare tare da kirkiro sabbin fasahohi. A cewar mista Schwab, yana da imanin cewa, matakan da kasar Sin ta dauka na sauya salon raya masana'antunta, da kara ingancin fasahohi a wannan fanni, za su taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China