in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman dake dauke akwatunan ajiye gawawwaki na sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura a Sudan ta Kudu ya isa Uganda
2016-07-16 13:13:09 cri
Jiya Jumma'a 15 ga wata, jirgin saman musamman dake dauke da akwatunan ajiye gawawwaki na sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura a kasar Sudan ta Kudu guda biyu ya isa filin jirgin sama na Entebbe na kasar Uganda, inda akwai hafsoshi na rundunar sojan kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta aike zuwa kasar Sudan ta Kudu dake tabbatar da yanayin tsaron wannan tawaga.

Haka kuma, tawagar aikin sojan kasar Sin da wasu ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Uganda sun je filin jirgin sama domin tarben su.

Kimanin karfe 4 da mintoci 15 na yammacin ranar Jumma'a, wani jirgin saman musamman da MDD ta shirya, dake dauke da akwatunan ajiye gawawwakin sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa kasar Sudan ta Kudu, watau Li Lei da kuma Yang Shupeng ya isa filin jirgin saman Entebbe na kasar Uganda, sa'an nan, kimanin karfe 6 da rabi na daren wannan rana, an kai akwatunan gawawwakinsu zuwa asibitin Mulago dake babban birnin kasar Uganda, watau Kampala.

Haka zalika, kafin tashin wannan jirgin saman daga kasar Sudan ta Kudu, rundunar sojan kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura a kasar Sudan ta Kudu ta gudanar da bikin ban kwana ga wadannan sojoji guda biyu, watau Li Lei da Yang Shupeng, wadanda suka mutu a yayin da suke gudanar da ayyukansu, kana, an gudanar da bikin a sansanin tawagar musamman na MDD dake birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu.

Bugu da kari, za a dawo da gawawwakin sojojin biyu gida cikin 'yan kwanakin nan masu zuwa.

A ranar 10 ga wannan wata, an kai harin bom kan wata motar sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake kasar Sudan ta Kudu yayin da suke gudanar da aiki a sansanin MDD dake kasar Sudan ta Kudu, wanda ya haddasa mutuwar sojojin Sin biyu, yayin da biyar suka ji rauni. (Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China