Jiya Alhamis, an kara kwashe wasu ma'aikatan kamfanin hakar mai na kasar Sin guda 93 daga Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu zuwa Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
A wannan rana da yamma, jiragen sama guda biyu da suka kwashe wadannan ma'aikata sun tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa na Juba, kuma suka isa a birnin Khartoum lami lafiya.
Mai kula da harkar kamfanin hakar mai na kasar Sin dake kasar Sudan ta Kudu Liu Yan ya bayyana cewa, tun bayan da hargitsin ya auku, sai kamfanin ya dauki matakai cikin gaggawa domin tabbatar da tsaron ma'aikatansa. Kawo yanzu ma'aikatai 51 suka rage a kasar Sudan ta Kudu, ban da wasu kwararrun kamfanin guda 6 da za su ci gaba da aiki a wurin, nan gaba za a kwashe duk saura zuwa birnin Khartoum.
A ranar 13 ga wata, Sinawa 71 aka kwashe daga Juba zuwa Khartoum cikin jirgin sama na musamma, yanzu Sinawa da suka isa Khartoum sun kai 164, kuma yawancinsu za su dawo kasar Sin.(Jamila)