A jiya Litinin, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da rikicin kasar Sudan ta kudu wanda ya hallaka jami'an kiyaye zaman lafiya biyu na kasar Sin, kana ya kalubalanci kwamitin sulhu na MDD da ya dauki matakai domin kawo karshen rikici da kuma kare rayukan fararen hula.
Ban Ki-Moon ya furta a hedkwatar MDD dake New York cewa, rikicin da ya barke a kasar Sudan ta kudu ya janyo koma baya ga yunkurin shimfida zaman lafiya a wannan kasa, da karfafa wahalhalun da ake fama da su, da kuma hallaka rayuka da dama. Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, ya kalubalanci kwamitin sulhu na MDD da ya dauki matakai ba tare da bata lokaci ba wajen hana jigilar makamai zuwa kasar Sudan ta kudu tare da kakkaba takunkumi ga mutanen dake zagon kasa ga yarjejeniyar shimfida zaman lafiya a kasar. A halin yanzu, tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta kudu na bukatar jiragen sama masu saukar ungulu dake dauke da makamai. Kwamitin sulhu na MDD na bukatar kara karfin wannan tawaga domin aikin kare rayukan mutane.
Bugu da kari, Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, ya ji mamaki sosai ga farmakin da aka kai wa fararen hula da jami'an kiyaye zaman lafiya na MDD. Ya kalubalanci shugabannin bangarorin biyu da rikcin ya shafa da su dauki matakan janye sojoji nan da nan domin tsagaita bude wuta da kawar da rikici.(Lami)