in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tura jirgin sama a Sudan ta Kudu domin kwashe sojojin da suka jikkata zuwa gida
2016-07-15 11:07:18 cri

Hukumar watsa labarai ta ma'aikatar tsaron kasar Sin ta bayyana cewa, bayan samun amincewa daga wajen shugaban kasar Sin Xi Jinping da kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jiya Alhamis wani jirgin saman ba da jinya ya tashi daga nan birnin Beijing zuwa kasar Sudan ta Kudu domin kwashe sojojin kasar Sin da suka samu raunuka dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Sudan ta Kudu. Kafin wannan, tawagar aikin da ke kunshe da wakilan da suka zo daga hukumomin kwamitin aikin soja da sojojin kasa da ma'aikatar harkokin wajen kasar da kuma wasu kwararrun ba da jinya ta riga ta isa kasar Sudan ta Kudu cikin jirgin saman soja.

A ranar 10 ga wata, agogon kasar Sudan ta Kudu, sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu adawa da gwamnatin kasar sun yi musanyar wuta a Juba, babban birnin kasar, a wancan lokaci, sojojin kasar Sin suna sintiri a kusa da sansanin 'yan gudun hijira cikin mota, ba zato ba tsammani, an harbi motar da suke ciki da igwa, a sanadin haka, sojojin Sin biyu sun rasa rayuka, yayin da biyar suka ji raunuka. Kawo yanzu, an riga an kai sojoji hudu da suka samu rauni mai tsanani zuwa asibitin kasar Uganba domin samun jinya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun mai da hankali sosai kan batun, kuma sun ba da umurnin tura tawagar aiki zuwa wurin da lamarin ya auku domin tattaunawa da gwamnatin kasar Sudan ta Kudu da tawagar sojojin wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar domin daidaita lamarin yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China