A cewar nazarinta, jahilci shi ne gishikin dake haddasa tashe tashen hankali da bambance bambance da ake nuna mata. Dalilin hake ne take baiwa ilimi babban muhimmanci wajen bunkasa 'yancin mata a Afrika.
Kuma a bangaren tarayyar Afrika, muhimmin makamin bunkasa ilimi shi ne yarjejeniyar Maputo. Karin takarda ga kundin Afrika kan 'yancin dan Adam, da aka rattaba hannu kansa a cikin watan Julin shekarar 2003 a yayin babban taron shugabanni da gwamnatocin kasashen Afrika a birnin Maputo na Mozambique.
Daya daga cikin sauye sauye na wannan yarjejeniyar Maputo, kamar yadda madam Wheeler ta tunatar shi ne muhimmancin da yake baiwa ilimi bisa ayyarsa ta 12 kan tilastawa masu fada a ji, na samarwa mata damar samun aiki da shiga harkokin kasa cikin adalci kuma ba tare da nuna bambanci ba. (Maman Ada)




