Kasar Rwanda dai na karbar bakuncin dandalin kungiyar AU daga ranar 10 zuwa 18 ga watan Yuli bisa taken "Shekarar 2016, shekarar 'yancin dan adam, tare da maida hankali musammun ma kan 'yancin mata". Da yake tsokaci gaban manema labarai a zaman taro da aka saba karo na 32 na kwamitin wakilan dindindin (PRC), Cherif Mahamat Zene, jakadan kasar Chadi dake Habasha, kana wakilin dindindin na kungiyar AU, yayi kira ga shugabannin Sudan ta Kudu dasu bullo da hanyar warware wannan rikici daga tushensa. (Maman Ada)




