Taken taron na wannan karo shine, "shekarar hakkin dan Adam, musamman lura da hakkin 'yan mata".
Kungiyar AU, ta sanar da hakan ga wakilan wasu kungiyoyin jama'a da na kasa da kasa, gami da yin bayani kan manyan batutuwan da za a tattauna a wajen taron karo na 27 na shugabannin kungiyar, kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar kungiyar a jiya Asabar.(Bello Wang)




