Fatima Haram Acyl, kwamishiniyar AU mai kula da kasuwanci da masana'antu, ta yi wannan kira ne a jiya Alhamis a yayin taron kolin AU karo na 27 a Kigali, babban birnin Rwanda.
Taron wanda ake gudanar da shi tsakanin ranakun 10 zuwa 18 ga wannan wata, mai taken "shekarar 2016 ta kare hakkin dan adam, da ba da fifiko ga hakkin mata".
Da take jawabi ga taron shugabannin kungiyar AU karo 29, Haram Acyl, ta shedawa 'yan jaridu cewar, kamar yadda kungiyar ta kuduri aniya kan muradunta na 2063 da sauran shirye-shirye, ta ce dole ne shugabannin Afrika da kwararru su duba yiwuwar cimma muradun kasuwanci maras shinge a nahiyar wanda wa'adinsa zai cika a shekara mai zuwa.
Kana ta bukaci ministocin kasuwanci na kasashen Afrika da su hanzarta cimma matsaya kafin karewar wa'adinsa a shekarar 2017. (Ahmad)




