Taron na bana wanda ake gudanarwa tsakanin ranakun 10 zuwa 18 ga wannan wata, taken taron na shekarar 2016 shi ne, "shekarar Afrika ta kare hakkin dan adam, tare da bada fifiko ga hakkin mata".
Babban jami'in kwamitin wakilai PRC, kuma jakadan jamhuriyar Chadi a Habasha, wakili na musamman a AU, Cherif Mahamat Zene, ya fada cewa sassauta dokoki game da cinikayya zai bunkasa cigaba wajen shigo da kayayyaki da fitar da dasu zuwa kasashen waje a nahiyar ta Afrika.
Ya kara da cewar babban kalubalen dake addabar hada hada tsakanin kasashen nahiyar shi ne, tsauraran dokokin dake haifar da koma baya ga sha'anin cinikayya a tsakanin kasashen na Afrika, don haka ya jaddada bukatar kawo sauyi ga wannan batu.(Ahmad Fagam)




