in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin a Sudan ta Kudu
2016-07-11 19:09:08 cri
A yau Litinin ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Lu Kang ya bayyana cewa, Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa sojojinta da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu, inda ta bukaci gwamnatin kasar Sudan ta kudu da ta gudanar da bincike kan wannan batu domin hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Lu Kang ya ce, Sin ta girgiza sosai kan wannan batu, ta kuma mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka mutu, tare da jinjinawa sojojin da suka jikkata da kuma iyalansu.

Ban da haka, rahotanni daga sansanin sojan kiyaye zaman lafiya na Sin a Sudan ta Kudu na cewa, wani soja daban da ya ji rauni a jiya Lahadi ya mutu ko da yake aka yi masa jiyya. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China