Hukumar harkokin watsa labaru ta ma'aikatar tsaron kasar Sin ta bayyana cewa, mukadashin shugaban ofishin harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar Su Guanghui ya jagoranci rukunin.
Rukunin zai nuna gaisuwa ga sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, tare da yin bincike ayyukan kiyaye tsaro a wurin da aka kai hari, da bada jagoranci ga sojojin kiyaye zaman lafiya wajen gudanar da aiki, da yin bincike kan yanayin sojojin da yanayin tsaro da ake ciki a can, da yin hadin gwiwa tare da tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta Kudu da gwamnatin kasar Sudan ta Kudu wajen daukar matakai don tabbatar da tsaron sojojin kiyaye zaman lafiya da gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata.
A ranar 10 ga wannan wata, an kai harin bom kan wata motar sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake kasar Sudan ta Kudu yayin da suke gudanar da aiki a sansanin MDD dake kasar Sudan ta Kudu, wanda ya haddasa mutuwar sojojin Sin biyu, yayin da biyar suka ji rauni. (Zainab)