in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin waje ta Sin ta yi kira ga bangarorin biyu na Sudan ta Kudu da su tsagaita bude wuta nan take
2016-07-11 21:09:33 cri
A yau Litinin 11 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang ya bayyana cewa, Sin tana mai da hankali sosai kan rikicin da ya barke a birnin Juba, hedkwatar kasar Sudan ta Kudu a kwanan baya, inda ta yi kira ga bangarorin biyu da abin ya shafa da su tsagaita bude wuta nan take, domin kaucewa karin mutuwa da jikkatar mutane.

Lu Kang ya ce, Sin ta yi kira ga bangarorin biyu da su tsagaita bude wuta kana su martaba yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar kasar da aka cimma, domin tabbatar da zaman lafiya a kasar cikin sauri, da kaucewa karin mutuwa da jikkatar mutane. Sin za ta ci gaba da taka rawar a zo a gani tare da kungiyar IGAD da sauransu wajen sa kaimi ga yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China