in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyin jama'a a Hongkong sun nuna kiyaya ga hukuncin da aka yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin
2016-07-15 10:35:43 cri
Wasu kungiyoyin jama'a na yankin musamman na Hongkong na kasar Sin, sun ba da sanarwar nuna kiyaya kan hukuncin da aka yanke dangane da batun tekun kudancin kasar Sin, inda suka nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Sin bisa matsayin da kasar ta dauka. A ganin wadannan kungiyoyin, wannan hukuncin da aka yanke sam ba zai yi tasiri ga ikon mallakar tekun kudancin kasar Sin da moriya a fannin teku da kasar Sin ke da su ba. Don haka, kungiyoyin dake sassa daban daban na yankin HongKong na kasar Sin sun bukaci kasashen dake nesa da yankin tekun kudancin kasar ta Sin da su daina tsoma baki kan wannan batun, da nuna girmamawa ga ikon mallakar harabar kasa da tabbatar da moriyarta kan teku na kasar Sin.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China