Hong Lei ya bayyana hakan ne yayin taron manema labaru da ya gudana a Talatar nan, bayan da Amurkan ta fidda wani rahoto mai kunshe da yanayin da ake ciki, game da manufofin gudanarwar yankin na Hong Kong.
Bugu da kari, kakakin ma'aikatar wajen kasar ta Sin, ya yi kira ga Amurka da ta martaba alakar dake tsakaninta da Sin, ta hanyar daina sanya baki cikin al'amuran cikin gidan Sin, duba da cewa hakan ka iya lahanta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin sassan biyu. (Saminu Hassan)