in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin yada labaru na Hongkong sun yi sharhi kan maganar da shugaba Xi Jinping ya yi game da makomar Hongkong
2014-12-28 17:16:10 cri
A ran 26 ga watan, yayin da yake ganawa da Leung Chun-ying, jami'in farko na gwamnatin yankin musamman na Hongkong na kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata a bunkasa tsarin siyasa a yankin Hongkong bisa doka kuma bisa hakikanin halin da ake ciki a yankin kamar yadda ya kamata. Sannan ya kamata a tafiyar da harkokin siyasa bisa ka'idojin kawo moriya a fannoni uku, wato, mazauna yankin za su iya jin dadin zama da yin aiki, za a iya kawo bunkasuwa da kwanciyar hankali a yankin, sannan za a iya tabbatar da moriyar ikon mulki da tsaro da kuma bunkasuwar kasar Sin gaba daya. Sakamakon haka, wasu jaridu da mujallun da aka wallafa a ranar 27 ga wata a yankin Hongkong sun ba da sharhi kan jawabin Xi Jinping, inda suka bayyana cewa, wannan jawabi yana da ma'ana sosai ga hakikanin halin da ake ciki a yankin Hongkong. Ya kamata a bunkasa harkokin siyasa a yankin Hongkong bisa doka, ta yadda za a iya kara karfin takara na yankin, da kuma tabbatar da bunkasuwa da kwanciyar hankali a yankin.

Jaridar Takungpao ta Hongkong ta bayar da wani sharhi a ranar 27 ga wata, inda ta bayyana cewa, gwamnatin tsakiya na kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin nuna goyon bayan kokarin aiwatar da shirin zabe a duk fadin yankin Hongkong a shekarar 2017 ne domin tabbatar da kawo moriya a wadannan fannoni uku. Gwamnatin tsakiya tana fatan mazauna yankin Hongkong za su iya kara jin dadin zama da aiki da samun ci gaba da kwanciyar hankali a yankin, har ma za a iya kara kare ikon mulkin kasa da tsaro da kuma bunkasuwar duk kasar Sin baki daya.

Haka kuma sharhin na jaridar Takungpao ta Hongkong ya nuna cewa, wannan ka'idar "kawo moriya a fannoni uku" ba ma kawai tana shafar zaben da za a shirya a shekarar 2017 ba, har ma tana shafar makomar yankin Hongkong a nan gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China