Bisa labarin da aka bayar, an ce, a kwanan baya, madam Daniel Russel, mai ba da taimako ga sakataren harkokin wajen kasar Amurka ta ce, babu hannun kasashen waje a lamarin mamaye wasu tituna a yankin Hongkong, sannan ba hannun kasar Amurka a tashin hankalin. Sabo da haka, bangaren Amurka ya nemi bangaren Sin da ya yi hakuri, kuma ya bar al'ummar Hongkong su bayyana abubuwan da suke son fada. Game da wannan furucin da madam Daniel Russel ta yi, madam Hua Chunying ta bayyana matsayin da bangaren Sin ke dauka. Kuma ta jaddada cewa, tabbatar da kwanciyar hankali da bunkasuwa a Hongkong cikin dogon lokaci ba ma kawai yana dacewa da moriyar kasar Sin ba, har ma yana dacewa da moriyar bangarori daban daban baki daya. Sabo da haka, bangaren Sin yana fatan sauran kasashe za su rika yin abubuwa kamar yadda suka fadi, kuma su cika alkawuransu, su rika yin abubuwan da za su taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali da bunkasuwa a Hongkong maimakon tayar da zaune tsaye. (Sanusi Chen)