Yayin taron, kungiyoyin masu masana'antu da ciniki na unguwoyi daban daban dake yankin isa zuwa kofar kwamitin tsara dokokin yankin kafin budewar taron, inda suka bayyana ra'ayinsu na nuna goyon baya ga shirin yin kwaskwarima kan tsarin siyasar yankin.
Kungiyoyin masana'antu da ciniki na unguwoyi daban daban na yankin Hongkong, da wakilan bangarori daban daban na yankin da yawansu ya kai kimanin 50, sun yi gangami a wajen babban ginin kwamitin tsara dokokin yankin, inda suka rika daga alluna masu dauke sa kalaman dake nuna bukatar baiwa jama'a damar zabar gwamnan yankin da kansu a shekarar 2017". Kaza lika masu gangamin sun mika wasikar bayyana ra'ayinsu ga mamban kwamitin tsara dokoki, inda suka bukaci membobin kwamitin da su bi ra'ayin yawancin jama'ar yankin, wajen zartas da shirin yin kwaskwarima kan tsarin siyasa. (Zainab)