in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkokin yankin Hongkong harkokin cikin gida ne na kasar Sin
2014-12-18 21:15:11 cri
A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, "yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Sin da Burtaniya" a shekarar 1984 ta tabbatar da ajandar dawowar yankin Hongkong hannun mahukuntar kasar Sin daga hannun mahukuntar Burtaniya. Sakamakon haka, bayan shekarar 1997, harkokin yankin Hongkong ya zama harkokin cikin gida na kasar Sin.

A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, akwai dan jaridar da ya yi tambaya cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 30 da kulla "yarjejeniya tsakanin Sin da Burtaniya", a ganinka, mene ne ma'anar wannan sanarwa ga yankin Hongkong na yanzu?

Mr. Qin Gang ya bayyana cewa, wannan "yarjejeniya tsakanin Sin da Burtaniya" da aka kulla a shekarar 1984, a bayyane ne ta shirya ajandar mika ikon mulkin yankin Hongkong da ayyukan da ya kamata a yi cikin lokacin wucin gadi, kuma ta kaddamar da ajandar dawowar yankin Hongkong hannun mahukunta kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata, an tafiyar da "Babban tsarin mulki" da manufofin "tsari iri biyu cikin kasa daya" da "mutanen Hongkong ke mulkin yankin Hongkong" a yankin Hongkong kamar yadda ake fata. Kana mutanen Hongkong ne ke tafiyar da harkokinsu da kansu. Sakamakon haka, yanzu yankin Hongkong yana ta samun bunkasuwa da kwanciyar hankali kamar yadda ya kamata. Muna cike da imani kan makomar yankin Hongkong na kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China