in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da wani sabon littafi kan hadakar Sin da Afirka ta fuskar al'adu a Abuja
2016-07-15 10:33:03 cri


Ranar Alhamis 14 ga wata ne, cibiyar al'adun kasar Sin dake birnin Abuja da sashin nazarin kimiyyar siyasa da alaka ta kasa da kasa na jami'ar Abuja sun yi hadin-gwiwa don shirya wani taron karawa juna sani dangane da hadakar kasar Sin da kasashen Afirka a fannin al'adu, da kuma kaddamar da wani sabon littafi a wannan fanni.

Wannan taron karawa juna sani gami da bikin kaddamar da sabon littafi ya samu halartar wasu shehunan malamai daga jami'ar Abuja, da jami'an gwamnatin Najeriya, tare kuma da jami'ai daga ofishin jakadancin Sin dake Najeriyar. Babban jigon taron shi ne, hadakar nahiyoyin Afirka da Asiya, musamman ma mu'amalar Sin da Afirka ta fuskar al'adu. Mahalarta taron sun tofa albarkacin bakinsu dangane da muhuimmancin mu'amalar al'adu tsakanin Sin da Afirka, da yadda al'ummar Najeriya da China za su ci alfanu daga irin wannan mu'amala.

Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, malami ne dake koyarwa a fannin kimiyyar siyasa da alaka ta kasa da kasa na jami'ar Abuja, wanda shi ne babban edita na sabon littafin da aka kaddamar mai suna hadakar yankunan Afirka da na sauran kasashen duniya. Ya bayyana ra'ayinsa game da muhimmancin cudanyar al'adu tsakanin Sin da Afirka.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China