in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron karawa juna sani don murnar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar kwaminisancin kasar Sin a Abuja
2016-07-01 09:17:26 cri

Kwanan baya, an yi wani taron karawa juna sani a cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, Najeriya, domin murnar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar kwaminisancin kasar Sin, wato babbar jam'iyya mai mulki a China.

Wannan taron karawa juna sani ya samu halartar wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya, da shehunan malamai masu nazarin tarihin kasar Sin daga jami'o'i daban-daban na Najeriya, ciki har da Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna, da tsohon ministan yada labaran Najeriya Malam Labaran Maku da sauransu. Wasu malaman jami'a sun gabatar da jawabinsu, inda suka bayyana ra'ayoyinsu game da tarihin jam'iyyar kwaminisancin kasar Sin, da gudummawar da wannan jam'iyya ta bayar a cikin tarihi, da kuma ayyukan da jam'iyyar take yi yanzu domin bunkasa zaman rayuwar al'ummar kasar Sin.

Daya daga cikin masu gabatar da jawabi, Dr. Sherrif Ghali Ibrahim, shi ne malamin dake koyarwa a fannin kimiyyar siyasa da alaka ta kasa da kasa a jami'ar Abuja. Ya bayyana cewa ya kamata a yi koyi daga babbar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China