in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kira da a guji aikata fyade a lokacin rikici
2016-06-20 11:21:46 cri
Babban magatakardan MDD mista Ban Ki-moon ya yi jawabi a ranar Lahadi domin bikin 'Ranar daina yawan yaki da aikata fyade a lokacin rikici', inda ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su mai da hankali wajen yakar yawan aikata laifukan fyade a lokutan da ake fama da rikici, sannan ya bukaci da a yanke hukunci kan wadanda suke aikata laifukan fyade domin kare mutuncin wadanda ake cin zarafinsu.

A cewar mista Ban, ana samun karuwar aikata fyade a lokacin rikici, kuma yadda lamarin ya yi tsanani ya ba mutane mamaki sosai. Wadanda suke aikata laifukan fyade suna lalata tsarin zaman al'umma, da tsoratar da jama'a, gami da kore su daga muhallinsu. Wannan lamarin, a cewar mista Ban, yana barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, da keta dokokin jin kai da na hakkin dan Adam, da gurgunta kokarin da ake na samun maslaha tsakanin al'umma da farfado da tattalin arziki bayan rikice rikice.

Ban da haka kuma, mista Ban ya ce, ana amfani da fyade a matsayin wata dabarar ta'addanci, inda kungiyoyin kamarsu IS da Boko Haram suke samun mutane su ajiye su da nufin shigar da su cikin kungiyoyin su ta hanyar wannan dabara. Haka zalika, suna amfani da lamarin don samun kudi. Yanayin da ake ciki ya sa 'yan mata, da wasu samari, da kananan yara maza da mata da aka sata suke samun mummunar illa, abin da ya shafi azabtar da jiki, da fyade.

A cewar babban magatakardan, idan an tuna da abubuwan da suka faru a wannan fanni, za a ga yadda aka sace dalibai mata fiye da 200 a Najeriya, da yadda kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi na gabas ta tsakiya suke tilastawa mata da su yi aure ko kuma su mai da su bayi, sun fi firgita mutane. Sa'an nan ya yi kira da a saki mutanen da ake tsare da su nan take, da kula da wadanda suka samu damar komawa gidajensu.

An fara bikin ne daga ranar 19 ga watan Yuni na shekarar 2015, inda babban taron MDD ya zartas da kudurin cewa, an amince da kowace ranar 19 ga watan Yuni ta zama 'Ranar yaki da fyade yayin rikici'. Wani rahoton da Ban Ki-moon ya gabatar a watan Afrilun bana ya sheda cewa, kungiyoyin masu makamai dake kasashen Afirka ta Tsakiya, Kodibwa, Congo Kinshasa, Mali, Somaliya, Sudan ta Kudu, da dai sauransu, gami da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi kamarsu IS da Boko Haram, suna ta aikata fyade yayin rikici.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China