Kungiyar wadda ta bayyana hakan a yau Talata cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce rukunin farko na wadanda za su fara amfani da fasfon sun hada da shugabannin kasashe da gwamnatoci na kungiyar,ministocin harkokin waje,wakilan din-din-din na kasashe mambobin kungiyar da ke zaune a hedkwatar kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar habasha.(Ibrahim)




