Taron wanda shi ne irinsa na farko da aka taba gudanarwa, an gudanr da shi ne a a farkon wannnan mako a hedkwatar hukumar ta AU dake Addis Ababa na kasar Habasha.
Manufar taron ita ne domin yin nazari game da muhimmancin samar da makamashi ta hanyoyi marasa illa ga bil adama don samar da lantarki domin samun bunkasuwa a yankunan gabashin Afrika.
A wata sanarwar da kwamishinan samar da ababan more rayuwa da lantarki na kungiyar AU Elham Ibrahim ya yi, ya yabawa kungiyar bisa shirya wannan taron a matsayin hanya da za ta karfafa gwiwa ga kamfanonin gwamnati da masu zaman kansu wajen nazarin hanyoyin samar da makamashi don inganta wutar lantarki a gabashin Afrika.
Elham ya ce yana da matukar muhimmanci a yi tunani game da samar da makamashi ta hanyoyi masara illa bisa la'akari da karuwar jama'a da ake samu a nahiyar ta Afrika.
Gary Quince, shugaban tawagar wakilan kungiyar tarayyar Turai EU a AU, ya ce idan aka yi la'akari da karuwar jama'a a nahiyar ta Afrika, zabin da ake da shi shi ne amfani da hanyoyin samar da makamashi a nahiyar ta Afrika domin samar da lantarki da kuma kiyaye muhalli. (Ahamd Fagam)




