in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata gudanar da aikin hadin gwiwa na shimfida bututun iskar gas zuwa kasashen Afrika
2016-07-12 10:40:22 cri
Gwamnatin Najeriya ta fada cewa, mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo zai jagoranci tawagar kasar zuwa taron koli na kungiyar tarayyar Afrika AU karo 27 wanda ake gudanarwa tsakanin ranakun 10 zuwa 18 ga wannan wata na Yuli a Kigali, babban birnin Rwanda.

Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja fadar mulkin kasar.

Ministan ya ce taron wata dama ce inda kasar zata gabatar da aikin shimfida bututun iskar gas na dala biliyan 20 daga Najeriyar zuwa Aljeriya karkashin hadin gwiwa na NEPAD.

Idan aikin ya kammala, za'a tura iskar gas kimanin cubic mita biliyan 30, daga birnin Warri na Najeriya zuwa Aljeriya ta ratsa kasar Nijer.

Sai dai kamfanin man kasar wato NNPC da Sonatrach na Aljeriyan ne zasu jagoranci aiki.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China