in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin biyu dake rikici a Sudan ta Kudu sun sanar da tsagaita bude wuta
2016-07-12 10:40:42 cri
A jiya Litinin, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ba da umarni cewa, sojojin gwamnatin kasar dake karkashin shugabancinsa za su tsagaita bude wuta da kansu a wannan rana tun daga misalin karfe shida na yamma agogon wurin.

A cikin wata sanarwar da aka gabatar ta gidan talebijin na Sudan ta Kudu, ministan sadarwa na Sudan ta Kudu, Michael Makuei Lueth ya bayyana cewa, duk hafsoshin sojojin kasar za su bi wannan umurni, su kula da sojojinsu, tare da ba da kariya ga fararen hula da dukiyoyinsu.

A wannan rana da dare, mataimakin shugaban kasar, Riek Machar ya bayyana ta bakin kakakinsa cewa, dakarun dake karkashin jagorancinsa su ma za su tsagaita bude wuta a wannan rana da dare da misalin karfe takwas.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China