Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi jawabi mai taken "Bunkasa duniya cikin hadin kai bisa daidaici da adalci", a gaban hukumar nazarin batutuwan kasa da kasa ta masarautar Birtaniya da hukumar nazarin tsare-tsaren kasa da kasa ta Birtaniya a safiyar ranar 18 ga wata a fadar shugaban yankin hada-hadar kudi da ke birnin London.
Mr Li ya bayyana cewa, irin matakin da Sin ke dauka na samarwa jama'arta biliyan 1.3 isashen abinci da kayayyakin yau da kullum, da matsuguni, har ma tabbatar da bunkasuwar masana'antu, sadarwa, garuruwa da birane, sha'anin noma cikin zamani, wannan ya kasance babban mataki tamkar wajen samun bunkasuwa da za a kushin kowa da kowa a tarihin Bil Adam. Hakazalika, Sin za ta ingiza samun bunkasuwar birane da garuruwa gaba daya, har ma za ta bi wata sabuwar hanyar raya masana'antu ba tare da gurbata muhalli ba wato samun bunkasuwa na bola jari.
Mr Li kuma ya jaddada cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka kan bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da nacewa ga tsarin bude kofa da kawo moriyar juna, kuma tana fatan hadin gwiwa da sauran kasashe, domin ba da gudunmawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya mai dorewa. Kuma game da ayyukan tada zaune tsaye, kasar Sin za ta cigaba da daukar matakai da suka dace, ta yadda za ta kiyaye zaman lafiyar duniya mai karko. (Amina)