in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afrika sun bukaci da a sake duba aikin tawagar MINUSS
2016-07-12 09:48:07 cri
Bayan kammala taronsu a ranar Litinin a birnin Nairobi, ministocin harkokin wajen yankin gabashin Afrika sun yi kira da a sake duba aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu (MINUSS), musammun ma kan kafa wani rukunin dakarun ko ta kwana, domin kawo karshen jin karar makamai a Juba.

Kwamitin ministocin hukumar cigaban kasa da kasa (IGAD), dake kunshe da kasashe mambobi bakwai, ya gudanar da wani taron gaggawa a Nairobi domin tattauna kan barkewar rikici a Juba.

Ministocin harkokin wajen kasashen Djibouti, Habasha, Kenya, Sudan, Sudan ta Kudu, Somaliya da Uganda, sun yi taro tun a ranar farko ta bude taron da kuma farkon jin karar makamai a Juba.

Ministocin sun yi kira ga mahukuntan Sudan ta Kudu da ya sake bude filin jiragen saman kasa da kasa na Juba da kuma mika aikin kiyaye tsaron shi ga tawagar MINUSS.

Haka kuma, ministocin sun yi kira da a bullo da wata takardar dake kunshe da batutuwa bakwai, musammun ma sake duba wa'adin MINUSS dake shafar batun kafa wani rukunin dakarun ko ta kwana.

A ranar Litinin, wani sabon fada ya barke a babban birnin Sudan ta Kudu, wato Juba, kwanaki biyu bayan wani barin wuta da ya halata sojoji biyar.

Daga karshe kuma, ministocin sun kira ga MDD da ta kara yawan sojojin MINUSS da aka dauko daga shiyyar domin kare Juba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China