Sanarwa ta ce, shugaba Deby Itno ya bayyana damuwarsa game da sake barkewar tashe tashen hankali a Sudan ta Kudu tare da kuma yin kira da a dakatar da bude wuta nan take.
Bisa bukata ta dalili, a matsayin shugaba mai ci na kungiyar AU, ya bukaci Alpha Oumar Konare wakilin dindindin na kungiyar AU a Sudan ta Kudu, da ya je wannan kasa domin ya isar da sakon damuwarsa kan bangarori masu gaba da juna.
A ranar Litinin da yamma, shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sanar da tsagaita bude wuta, 'yan kwanaki kadan bayan wani gumurzu tsakanin sojojin gwamnatin kasar da dakaru masu biyayya ga mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar. (Maman Ada)