in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar game da hukuncin da kotu ta yanke kan batun tekun kudancin Sin bisa bukatar kasar Philippines
2016-07-12 19:34:22 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa, ba ta amince ba kuma ba ta yarda da sakamakon hukuncin da kotu ta yanke a yau bisa bukatar Jamhuriyar kasar Philippines kan batun tekun kudancin kasar Sin ba.

A ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2013 ne, tsohuwar gwammatin Jamhuriyar kasar Philippines bisa radin kanta ta shigar da kara game da takaddamar da ke tsakaninta da kasar Sin game da batun tekun kudancin Sin. Amma a ranar 19 ga watan Fabrairun shekarar 2013, gwamnatin kasar Sin ta ayyana cewa, ba ta amince da wannan mataki na kasar Philippines ba kuma ba za ta halarci zaman kotun ba, kuma tun wannan lokaci ta sha nanata wannan matsayi da ta dauka kan wannan batu.

A ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2014, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takarda wadda ta ke bayyana matsayinta game da hurumin kotun da kasar Philippines ta kirkiro game da wannan batu, tana mai bayyana cewa, matakin da kasar Philippines ta dauka ta neman kafa wannan kotu ya sabawa yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, sannan ya keta yarjejeniyar teku ta MDD, da kuma baki dayan ayyukan shiga tsakani na kasa da kasa, kuma wannan kotu ba ta da 'yancin yanke hukunci kan wannan batu.

A ranar 29 ga watan Oktoban shekarar 2015, wannan kotu ta bayar da sanarwar damar sauraron wannan kara. Amma nan da nan gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa, ba za ta amince da wannan mataki na kotu ba, kuma ba ta da hurumin shiga wannan lamari. Matsayin kasar Sin kan wannan batu a bayyane yake kuma ba zai canja ba.

Matakin da kasar Philippines din ta dauka na gabatar da wannan batu a gaban kotu, ko kadan bai dace ba. Kuma hakan ba zai taimaka wajen warware takaddamar dake tsakanin Sin da Philippines ba, ko kuma ya taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun kudancin kasar Sin. Haka kuma wani yunkuri ne na take 'yancin mallakar yankuna da teku na kasar Sin da kuma muradunta a yankin tekun kudancin kasar. Bugu da kari, kafa wannan kotu bisa bukatar Philippines shi kansa ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kotun da kasar Philippines ta nema a kafa bisa radin kanta ba ta yi la'akari da cewa, maganar da ake batu a kai shi ne batutuwan 'yancin mallakar yankuna da shata iyakan teku, maimakon haka sai bisa rashin sani ta nemi yanke hukunci ta hanyar amfani da damar sassanta takaddama wanda tuni kasashen Sin da Philippines suka yi hakan, kuma bisa rashin sani hakan ya sabawa matakin sasantawa tsakanin sassan biyu kai tsaye, har ila bisa rashin sani ta yi watsi da yarjejeniyar da Sin ta cimma karkashin doka ta 298 na dokokin teku na MDD, inda ta zabi tsibirai da tsaunukan da ake batu a kansu daga cikin baki dayan tsibiran da ke cikin tekun kudancin Sin, kuma baki daya ta sanya su karkashin dokokin teku na MDD.

Hukuncin kotun da yadda ta tafiyar da wannan batu, ya sabawa ayyukan sasantawa na kasa da kasa, kuma ya kauce daga dalilin kafa dokokin teku na MDD har zuwa yadda ake kokarin sassanta takaddama cikin lumana, kuma wannan mataki ya take 'yancin kasar Sin na mallakar yankunanta.

A saboda haka, gwamnatin kasar Sin ta sake nanata cewa, game da batutuwan da suka shafi warware kan iyakokin kasa da na teku, kasar Sin ba ta amince da duk wani mataki na shiga tsakani daga wani bangare da wannan batu bai shafa ba, ko wani mataki na tilastawa kasar Sin. Gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da martaba dokokin kasa da kasa da kuma ka'idojin da suka shafi hulda da kasa da kasa kamar yadda yake kunshe cikin dokokin MDD, ciki har da manufofin mutunta yankunan kasa da sassanta rikici ta hanyar lumana, da ci gaba da tuntubar sauran kasashe da batun shafi wajen daidata batutuwan da suka shafi batun tekun kudancin kasar Sin ta hanyar tattaunawa bisa tushen mutunta bayanan tarihi kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar a yanikin tekun kudancin kasar Sin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China