in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun da aka kafa a Hague ba ta da ikon yanke hukunci kan batun tekun kudancin Sin
2016-07-12 14:03:24 cri

A yau Talata ne ake saran kotun yanke hukunci da ke Hague, za ta yanke hukunci kan batun tekun kudancin Sin bisa bukatar kasar Philippines. Shugaban cibiyar yanke hukunci ta kasa da kasa ta Hongkong Zheng Ruohua ya bayyana a yankin Hongkong a jiya Litinin cewa, bisa yarjejeniyar dokar teku ta MDD, kamata ya yi bangarorin biyu da rikicin ya shafa su yi shawarwari tukuna, amma kasar Philippines ta nemi da a yanke hukunci kan batun ba tare da yin shawarwari ba, ban da haka kuma, saboda yarjejeniyar dokar teku ta MDD ta kare 'yancin kasashen duniya, shi ya sa, kotun hukunci ta Hague ba ta da ikon yanke hukunci kan batun tekun kudancin Sin.

Ban da haka kuma, Zheng Ruohua ya kara da cewa, kasar Sin ta kulla sanarwar bangarori daban daban da batun tekun kudancin Sin ya shafa tare da kasashen kawancen kudu maso gabashin Asiya a shekarar 2002, inda suka cimma matsaya daya kan daidaita batu ta hanyar yin shawarwari. A halin yanzu, ana ci gaba da aiwatar da wannan sanarwa, a saboda haka, dukkan bangarorin biyu ba su da ikon neman yanke hukunci a kan batun, shi ya sa, kotun ta Hague ba ta da ikon daidaita wannan batu bisa doka.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China