in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga sojojin kasar Sin dake gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2016-07-11 11:44:19 cri
Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta tabbatar a ranar 11 ga wata da cewa, an kai hari ta igwa kan wata mota mai sulke ta bataliyar sojojin wanzar da zaman lafiya Sinawa dake kasar Sudan ta Kudu, a ranar Lahadi, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa ran wani sojan kasar Sin, da raunata wasu 6, yayin da 3 daga cikinsu suka samu raunuka masu tsanani.

Cikin sanarwar da ofshin watsa labarai na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bayar, an ce an kai hari ga sojojin ne lokacin da suke gudanar da aikin tsaron mafakar 'yan gudun hirjira. A nata bangaren, rundunar sojan kasar Sin ta nuna kaduwa game da faruwar hari, kuma ta yi Allah wadai da mummunan harin da aka kai. Bangaren rundunar ta nuna juyayi ga rasuwar sojanta, kuma ta jajantawa iyalan wadanda suka samu raunuka.

Bayan abkuwar harin, rudunar sojojin kasar Sin ta kaddamar da shirin ko ta kwana nan take, kana ana kokarin ceton rayukan sojojin da suka ji rauni, gami da kara tsaurara matakan tsaro a wurin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China