A cikin sanarwar, da babbar murya kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki, yana mai jaddada cewa, kai hari kan farare hula da sansanin hukumomin MDD da ma'aikatan MDD tamkar aikata laifin yaki ne. Don haka dole a gurfanar da wadanda suka kai harin a gaban kotu.
Dadin dadawa, a cikin sanarwar, kwamitin sulhun MDD ya jaddada muhimmancin ba da kariya ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD da wuraren MDD da ke kula da lafiyar fararen hula a wurin. Ya ce kwamitin sulhun zai yi la'akari da kara tura sojoji zuwa tawagar musamman ta MDD dake Sudan ta Kudu. (Fatima)