in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Serena ta lashe kofin gasar Wimbledon
2016-07-13 10:02:17 cri
Shahararriyar 'yar wasan tennis Serena Williams ta lashe kambin gasar Wimbledon a karo na 7 a wasan karshe da ta buga tare da Angelique Kerber a Asabar da ta gabata, inda ta lashe Kerber din da ci 7 da 5, da ci 6 da 3. Wannan nasara ta sa 'yar wasan da ke matsayin farko a jadawalin gasar tennis ta duniya na samun kambinta na 22 a manyan wasannin kasa da kasa, daidai da wata bajintar da aka taba kafawa a tarihin wasan.

Bayan da ta lashe gasar Wimbledon ta shekarar da ta gabata, 'yar wasan ta dade tana tsayawa kan lashe manyan wasanni 21, kuma bata samu damar kara kambi daya ba, sai dai zuwa yanzu wannan 'yar kasar Amurka ta kawo karshen wannan yanayi maras kyau da ya dade yana damun ta, ta hanyar sake kwaton kambin gami da samun kambunan da yawansu ya yi daidai da bajintar da Steffi Graf ta kafa.

A wannan wasa, Serena ta samu matsin lamba sosai daga abokiyar karawarta Kerber a wani wasan da aka kwashe mintuna 81 ana gudanar da shi a shahararren filin wasa na Centre Court. Sai dai sannu a hankali 'yar wasan dake da matsayi na 4 a teburin kasar Jamus ta fado cikin yanayin shan kaye, ganin yadda 'yar wasan Amurka ta samar da kwallon Winners 39 gami da na Aces 13.

Da wannan nasara kuma, ita Serena ta yi ramuwar gayya ga Kerber, wadda ta lashe Serena a wasan karshe na gasar Australian Open wanda ya gudana a watan Janairun bana. Serena ta yi murna kwarai da gaske yayin da take tafiya a kewayen filin wasan Centre Court bayan da ta samu kyautar kudin da yawansa ya kai Fam miliyan 2.

Sai dai kyautar da ta fi daraja a idon 'yar wasan ita ce, ta sake tabbatar da matsayinta na 'yar wasa mafi kwarewa a wannan fanni, a wani lokacin da wasu mutane ke nuna shakku kan karfin 'yar wasan mai shekaru 34 a duniya wajen samun nasara, musamman ma ganin yadda ta yi kokarin neman lashe kambunan manyan wasannin kasa da kasa ba tare da samun nasara ba a shekarar da muke ciki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China