in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya Bolt cikin kungiyar Jamaica don halartar gasar Olympics a Rio
2016-07-13 10:00:05 cri
An sanya Usain Bolt, wanda ya lashe lambobin zinare a wasannin Olympics har sau 6, cikin kungiyar 'yan wasan kasar Jamaica, wadda za ta halarci Olympics din da zai gudana a birnin Rio na kasar Brazil a wannan shekara. Jami'ai masu kula da aikin wasanni na kasar Jamaica sun tabbatar da haka a ranar Litinin.

Kafin haka akwai damuwar da aka nuna cewa watakila Bolt ba zai samu damar halartar gasar ba, ganin yadda ya samu rauni a jijiyar kafarsa, yayin jarrabawar da aka yi a kasar Jamaica don tabbatar da 'yan wasan da za su halarci Olympics a madadin kasar.

Sai dai a karshe hukuma mai kula da aikin da ya shafi Olympics ta kasar Jamaica ta ba shi damar halartar gasar, bayan da aka duba lafiyar jikinsa sosai. Don haka, wannan dan wasa mai shekaru 29 a duniya zai yi kokarin kare kambunan da ya samu a wasannin Olympics da suka gudana a Beijing na kasar Sin a shekarar 2008, da London na kasar Birtaniya a shekarar 2012.

Yanzu Bolt yana samun jinya a kasar Jamus karkashin kulawar da wasu kwararrun likitoci suke yi masa. Sa'an nan a ranar Lahadi ya sanya wani bidiyon a shafinsa na internet, inda ya tabbatarwa magoya bayansa cewa, zai halarci wata babbar gasar da za ta gudana a birnin London a ranar 22 ga watan Yuli.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China