in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boateng na kulob din Bayern zai murmure kafin fara sabuwar kakar wasa
2016-07-11 15:14:20 cri

Dan wasan bayan kulob din Bayern Munich na kasar Jamus Jerome Boateng zai samu damar halartar wasanni a farkon watan sabuwar kakar wasa, duk da samun raunin da yayi a cinyarsa, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwar da kulob din ya fitar a ranar Asabar da ta gabata.

Dan wasan mai shekaru 27 a duniya, ya gurgunta sakamakon raunin daya samu a jijiyarsa ta cinyar dama, a yayin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai UEFA EURO, inda kungiyar Faransa ta lashe kungiyar Boateng ta kasar Jamus da ci 2 da nema.

Duk kuwa da haka, an ce halartar Boateng a daya daga cikin wasannin farko da za a buga tsakanin Bayern Munich da Werder Bremen karkashin tsarin gasar Bundesliga a ranar 26 ga watan Augusta mai zuwa, ta kusan tabbata, ganin yadda dan wasan zai murmure sosai kafin lokacin, in ji sanarwar kulob din.

Dan wasan nan wanda ke da jinin dan kasar Ghana, ya taka rawar gani a wasanin da suka gudanar a wannan gasar cin kofin nahiyar Turai, ya kuma kaura zuwa Bayern Munich daga Manchester City a shekarar 2011, inda ya fara zama wani babban dan wasan baya. Zuwa yanzu ya halarci wasanni 124 tare da buga kwallaye 3 cikin raga a madadin Bayern Munich.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China