in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shandong Luneng ya kulla kwangila da Cisse
2016-07-13 09:59:00 cri
Daya daga cikin fitattun kuloflikan kasar Sin Shandong Luneng ya sanar a ranar Asabar da ta gabata da cewa, Papiss Cisse ya kaura zuwa kulob din daga Newcastle United.

Dan wasan gaban, dan asalin kasar Senegal mai shekaru 31 a duniya ya taba taka leda a kasashe daban daban kamarsu Faransa, Jamus, gami da Birtaniya. Da ma ya sauya shekarsa daga SC Freiburg zuwa Newcastle United a watan Janairun shekarar 2012. Kafin haka kuma ya yi shekaru 4 da rabi yana buga kwallo a kulob din Magpies karkashein tsarin gasar Premier League na kasar Birtaniya.

Sai dai kulob din Shandong Luneng baya cikin wani yanayi mai kyau, ganin yadda ya ci kwallaye 7 yayin da aka ci shi kwallaye 16 a wasanni 10 da suka gabata, lamarin da ya sanya shi kasancewa cikin yanayi na yiwuwar rage matsayinsa.

Cisse ya buga kwallaye 44 cikin raga a wasanni 131 da ya shiga a madadin Magpies. Haka kuma shi ne dan wasa dan asalin Afirka da ya fi buga kwallaye cikin raga a kakar wasa na tsarin gasar Bundesliga, bajintar da ya kafa a kasar a wasannin 2010/11, lokacin da ya buga kwallaye 22 cikin raga a madadin kulob din SC Freiburg. Hakan ya kasance dalilin da ya sa koci mai horar da 'yan wasan kulob din Luneng daga kasar Jamus Magath yake son kulla kwangila da Cisse.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China