in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Portugal na cigaba da murnar cin kofin zakarun nahiyar Turai na farko da ta samu
2016-07-12 15:52:53 cri


Bayan da kungiyar wasan kasar Portugal ta doke takwararta ta kasar Faransa da ci 1 da nema a wasan karshen gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a ranar Lahadi, masu sha'awar wasannin kwallon kafan kasar suna ta shagulgula domin murnar wannan babbar nasarar da kasarsu ta samu.

Bayan da 'yan wasan kungiyar suka koma kasarsu ta Portugal , shahararren dan wasan kunigyar Cristiano Ronaldo ya nuna kofin da suka samu ga jama'a 'yan asalin kasar Portugal gami da masu goyon bayan kungiyarsu.

Ronaldo ya ce, 'dukkanku, 'yan asalin kasar Portugal, da 'yan wasan kungiyarmu, da babban kocinmu, dukkannin ku kun cancanci yabo game da wannan nasara, gami da wannan kyauta.'

A wasan da ya gudana tsakanin Portugal da Faransa a ranar Lahadi, an dauki Ronaldo zuwa gefen filin wasa sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa, amma duk da haka kungiyarsa ta lashe ta Faransa cikin karin lokacin buga wasan da aka bayar, inda shi Eder ya buga kwallo cikin raga a mintinu 109 da fara wasan.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China